2 Thessalonians 2

1Yanzu game da zuwan Ubangijinmu Yesu Almasihu da taruwarmu domin kasancewa tare da shi; muna rokonku yan’uwa, 2kada kuyi saurin damuwa ko ku gigice saboda wani ruhu ko kuma sako ko kuma wasika da ta yi kamar daga wurin mu, da ke cewa ranar zuwan Ubangiji ta rigaya ta zo.

3Kada wani ya yaudare ku ta kowace hanya. Domin wannan rana baza ta zo ba sai fandarewar nan ta zo kuma an bayyana mutumin tawayen nan wato dan hallaka. 4Wannan shi ne wanda ya ke gaba, yana kuma daukaka kansa fiye da duk abin da ake kira Allah ko kuma ake bautawa. Sakamakon haka yana zama a kursiyin Allah har ma yana cewa shine Allah.

5Baku tuna ba lokacin da nake tare daku na gaya maku wadannan abubuwa? 6Yanzu kun san abinda ke tsaida shi, domin a bayyana shi a lokacin da ya dace. 7Ko yanzu asirin take shari’a ya na aiki, sai dai a kwai wanda ke tsaida shi yanzu har sai an dauke shi.

8Sa’anan za’a bayyana dan tawayen, wanda Ubangiji Yesu zai hallaka shi da numfashin bakinsa. Ubangiji zai mayar da shi ba kome ba ta wurin bayyanuwar zuwansa. 9Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga aikin shaidan da dukan iko, alamu, da al’ajiban karya, 10da kuma dukan yaudara ta rashin adalci. Wadannan abubuwa za su zama ga wadanda suke hallaka, saboda ba su karbi kaunar gaskiya ba domin su sami ceto.

11Saboda wannan dalilin Allah ya aiko masu da sabani, saboda su yarda da karya. 12Sakamakon shine dukkan su za’a yi masu shari’a, wato wadanda ba su yarda da gaskiya ba suna kuma jin dadin rashin adalci.

13Amma muna masu godiya kulluyaumin ga Allah domin ku, yan’uwa wadanda Ubangiji yake kauna. Ubangiji ya zabe ku a matsayin yayan fari don ceto cikin tsarkakewar Ruhu da gaskatawa da gaskiya. 14Wannan shine abinda ya kira ku gare shi ta wurin bishararmu domin ku sami daukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 15Saboda haka yan’uwa, ku tsaya da gaske. Ku rike al’adun da aka koya maku, ko ta kalma ko kuma ta wasikarmu.

16Yanzu bari Ubangiji Yesu Almasihu da kansa, da Allah Ubanmu wanda ya kaunace mu ya ba mu madawwamiyar ta’aziya da gabagadi mai kyau domin gaba ta wurin alheri, ya ta’azantar da ku ya kuma gina zuciyarku cikin kowane aiki mai kyau da kalma.

17

Copyright information for HauULB